Social & Communication Difficulties
1. Difficulty making eye contact
A misali idan ana lecture, lecturer yana explanation ko ma wani yana mun bayani wani abu, kallon cikin idon mutum yana mun wahala kawai wani iri. Idan nayi forcing din kaina na holding eye contact din, kawai wani zafi. kawai ba dadi.
2. Finding it hard to talk to other people / not knowing what to say
A misali idan na hadu da wani maybe a taro ko kuma muna jiran wani ya bamu wani abu, idan naga alamun ya kamata mu gaisa, nayi sallama ya amsa, shikenan bana cewa komi saboda bansan me zance ba. In har ba wani question zan tambayeshi ba, babu abun da yake zuwa kaina.
Idan shikuma yayi magana, mostly question, dana bashi amsa shikenan.
Akwai sanda naje asibiti zanga likita. Daya daga cikin nurses din ta gane ni amma ni ban gane taba ba. Tace kayi Iman ko (Secondary school) daya mu kayi? Sai nace ehh. Sai “tace haba nifa ince kuna senior class”. banji abunda tace sosao ba. Sai nace okay muna junior class kuna senior. Sai tace a'a kune senior. Sai wata nurse din ta katse mu ta tambaye ni regarding abunda ya kawoni. Shikenan, daga nan nayi shiru. I don't know what else to say so conversation din ya tsaya.
i think abunda yake hanan magana nake freezing shine, bana so na fadi wan abunda ba daidai ba ko kuma idan bana magana im fully aware of the environtment kamar ina protecting kaina ne . saboda acikin mutane musanman mata kamar ina shaking haka yin magana kamar yana exposing hakan so i have to stay still and calm.
3. Feeling awkward in social situations / fear of being judged
Idan ina wani wuri saboda wani reason kamar wani ze bani abu ko ni zan bada abu, nayi magana akace na jira, zanyi zama na ko banyi magana ba, ba abunda zanji.
Amma idan taro ne ko wani social gathering, sai naji yaya mutane suke kallona.
"Is this guy creepy?"
Kuma idan nayi magana. saboda banajin dadin zama a irin wannan situation din sannan magana na ba wasa, mutane zasu daukeni boring ko awkward. saboda mutane da yawa sunce im so seriouse nima kuma nasan hakan
On some level nasan hakan shiyasa bana zuwa family meetings haka, saboda ina behaving like I really need them to like me. Banason yadda nake behaving.
4. Difficulty understanding sarcasm or what people mean
Bana fahimtar abu kamar sarcasm haka.
A misali muna picnic, wani course mate dina yaga kamar ni kadai ne ban cinye abinci na duka ba, ga kashin kaza na bari.
Bayan an tashi za ayi hoto sai yace:
"Adnan ka kadai ne dan gayu , bazaka bamu kunya ba."
Ban san meye zance masa ba. Ban san ko da gaske yake, he admires me , ko sarcasm ne. Kawai nayi murmushi nayi shiru na wuce. wanda abune wanda nakeyi sosai kawai nayi murmushi , idan bansan me zance ba ko bangane abunda mutane suke nufi ba
5. Saying things that seem normal to me but strange to others
Ina fadan wasu abubuwan that are odd to people but normal to me.
A misali shekaru 4 zuwa 5 baya muna chat a group da classmates ana joking, kamar mu uku zuwa hudu na manta most of the details din.
Wata sunanta Amina tace zata zo gidanmu ko tayi me
Sai nace:
"Akwai kare dai a gidanmu."
Agurina wannan normal ne.
Amma agurin mutane ba haka bane.
irin haka yana faruwa dayawa
6. Worrying about saying the wrong thing
Idan zanyi magana da mutane ina tantance abunda zance saboda banaso na fadi abunda ze bata musu rai, wanda ba niyya ta bane na batawa mutum rai.
Misali lokacin da ina SS2 ina zuwa makaranta da machine.
Chemistry teacher dinmu ma yana zuwa da machine amma nawa yafi nasa kyau.
Daidai munzo parking sai yace wani abu wanda na manta kamar complementing din machine dina da kuma degradin din nashi inaga abunda yayi kenan.
Sai nace:
"Ai haka abun yazo."
Expression da reaction dinsa ya nuna min na bata masa rai.
Agurina babu abunda nayi.
Amma agurinsa nayi masa wani abu da ya bata masa rai.
7. Showing few emotions / difficulty expressing myself
Mutane suna yawan cemin miskili, reserved.
Yawanci idan ban gane abu ba ko bansan me zance ba, murmushi kawai nayi shiru. ko nace ehh gsk ko kuma Allah sarki
9. Difficulty explaining my thoughts
Bana iya explaining abu.
Akwai lokacin da naje hostel gurin abokina ana maganar Money Heist.
Daya daga cikinsu yace bai kalla ba.
Sai suka tambaye ni ko na kalla, da kuma yaya dadin series din yake don yayi convincing dinshi yaje ya kalla.
Nakasa explaining.
Kawai abunda zan iya cewa shine:
"Anyi planning heist, anyi executing.”
ina son film irin wanna wanda anyi planing ahead duk wani scenario even failure is a success
10. Difficulty making and maintaining friendships
Na fahimci kamar ni nake pushing people away not to be my friends.
Ina tuna gesture na mutane dayawa suna cewa:
"Hey, let's be close."
Amma daga nine i dont know why .
Tun ina yaro, jumping nake daga wannan friendship zuwa wani.
A misali, abokaina na yanzu, kafin mu zama abokai, na fara abota da yayansu ko kannansu.
Abokan da na shigo university tare dasu, ba su bane abokaina yanzu ba.
11. Avoiding people to avoid conversation
Idan naga mutane kawai bana son haduwa dasu saboda bana son yin magana.
A misali Akwai tutor dina lokacin ina level 200 yana mana Maths tutorial.
Saboda ina ganewa sosai, muna mutunci da juna har muka yi exchanging phone numbers.
Unguwa daya muke yalwawa.
Ina yawan zama a bakin titi ina karatu a waya.
To sunzo wucewa ni kuma ina zaune kawai se na dauke kaina ko nayi kasa da kaina nayi hoping be ganni ba.
Irin haka yana faruwa dayawa da mutane dayawa.
kawai banason yin magana.
se inyi sauri in tafi don karma sunganni har muyi magana.
12. Difficulty with changes to plans / expecting people to keep agreements exactly
Idan mukayi da mutum zamu hadu karfe goma na safe, ko kuma nace zan kasance wani gari ranar kaza, hankalina baya kwanciya.
Ji nake dole ne na kasance a wurin daidai lokacin.
Bana son African time.
Idan muka ce karfe goma, sai mutum yazo goma da minti goma, nakan ji haushi sosai.
Kamar ya karya alkawari.
Kamar ya ci amanata.
13. Feeling guilty when I cannot keep my own plans
Akwai wani abokina.
Mun shirya cewa zan koma Duste ranar Saturday saboda zan taimaka masa da project proposal dinsa.
Sai ranar Thursday naje wajen likitan hakori.
Ranar Friday kuma za’a cire min hakori.
Ya zama ba lallai na iya komawa ranar saturaday ba
Se nake jin wani iri ian banje ranar saturaday ba
Ya zama kamar nayi karya kenan
Ban masa adalci ba nace zanzo guri kaza amma banjeba
Kamar yadda banaso ayimin hakan banaso nayiwa wani
14. Difficulty expressing genuine emotional reactions
Idan muna magana da mutane, bansan me yasa ba amma faking expressions nakeyi.
A misali idan mutum yana bani wani labari da yake ganin abin dariya ne, amma agurina ba abin dariya bane, wani lokacin sai nayi fake laugh kawai don na nuna masa ina engaging da conversation.
Ba saboda abin ya bani dariya ba.
Ko da mutum bai gane ba, ni nasan fake laugh ne.
Misali
Ranar Thursday hakan ya faru.
Mamanmu tana bani wani labari.
An ga wani tsohon hoton kanina lokacin yana yaro.
Lokacin da shi da kanwata suke dawowa daga makaranta, Mamanmu tana sauraron shirin rediyo "Duniyarmu A Yau."
Sai suke rera taken shirin(Duniyarmu ayau )daidai lokacin da Mamanmu take sauraron shirin.
Agurina labarin bai bani dariya ba.
Amma saboda na nuna ina engaging da conversation, sai nayi fake laugh.
Ko da Mamanmu bata gane ba, ni nasan fake laugh ne.
hakan yana faruwa da mutane dayawa wasu ma suna spoting wannan fake laugh din.
Wani abokina ma yace dalilin da yasa nake shiru na rasa abunda zan fada shine saboda because im predictable, nace yayi explaining. exact words dinshi " im always looking for validation." and i think its true.